Monday 23 August 2010

Wasu na Shan Ruwan Bunu a Watan Azumi, Wasu na Shan Kindirmon Kwali


Watan Azumi wata ne mai alfarma ga dukkanin Musulmi a koina a cikin duniya. Kuma yau, a kwana a tashi, gashi har wata yana neman rabawa. A duk tsahon wannan watan BBC Hausa tana kawo rahotanni da sakonnin “shan ruwa daga masu sauraron mu”.

Wasu sun aiko mana da tambaya suna cewa mecece fa’ida ko hikimar kawo sakonnin “shan ruwa daga masu sauraron mu?” To lallai ga wanda bai kalli lamarin cikin zurfin tunani ba zai ga tamkar ba wani abu ba ne illa kawai kawo mutane suna cewa sun ci kaza sun sha kaza. A saboda haka kenan wannan ba abu ne mai mahimmanci ba.

Sai dai ni kuwa ba haka nake kallon abun ba. Ina kallon sa ne daga fannin launin abincin da mafi yawan jama’ar mu ke ci a wannan wata mai tsarki bayan sun kamalla ibadar su da magariba.

Kowa dai ya wuni da azumi, zai so ya yi buda baki da dan abun marmari da kuma ababen gina jiki wadanda zasu mayar da gurbin abunda aka rasa a yayin azumin. Sai dai sauraron irin abunda da mafi yawan al’ummar Hausawa ke shan ruwa da su, abu ne dake kawo hawaye a ido.

“Ni dai yau na sha ruwa da ruwan bunu da rama; yau na ci dabino da kunun kanwa, illa iyaka; ni dai na sha ruwa da dan-wake da mai da yaji, iyakar abunda Allah ya hore min kenan, Allah ya nuna mana gobe lafiya!”

Wadannan sune kadan daga dubban sakonnin da BBC Hausa ke samu a kowanne dare. Me sakonnin suke nuna mana? Lallai suna yin nuni ne da irin wahalar da jama’a suke ciki a kasar mu. Kuma yayinda miliyoyi ke shan “ruwan bunu” wasu ‘yan tsiraru kuwa suna shan kindirmon kwali mai sanyi da naman kaji.

Nigeria dai ba kasa ce matalauciya ba. Amma kuma jam’a na cikin halin matanancin talauci. An san dalilan da suke janyo talaucin: rashin shugabanci na-gari, rashawa, almundahana, rashin adalci da tsananin san-kai. Kididdgar Majalisar Dinkin Duniya na cewa mafi yawan ‘yan Nigeria na rayuwa ne akan kasa da Dala daya – wato kasa da Naira 150 - a rana.

A wannan lokaci na ibada kamata yayi mu kara tunani a game da halayyar mu ko Allah zai ji tausayin mu. Mu gyara halayen mu sannan kuma mu roke Shi Ya ba mu shugabanni masu tausayin talakawa, wadanda zasu fitar da al’ummar mu daga kangin talauci.

A sha ruwa lafiya!